Rahotanni sun bayyana cewa fadar shugaban kasar ta mikawa majalissar sunan Godwin Emefiele, dake matsayin babban manajan daraktan bankin Zenith domin tabbatarwa.
Da zarar an tabbatar da Emefiele zai ci gaba da jagorantar babban bankin kasar CBN, gabanin karewar wa'adin aikin Sunusi Lamido wanda zai cika a ranar 2 ga watan Yuni mai zuwa.
Har wa yau, shugaban kasar ya mika sunan daraktan First Bank Adelabu Adebayo, domin nadinsa a matsayin mataimakin gwamnan babban bankin kasar. Kafin wadannan sauye-sauye, yanzu haka babbar mataimakiyar shugaban babban bankin Sarah Alade ce za ta rike mukamin gwamnan bankin na CBN.
Wata sanarwar da fadar shugaban Najeriyar ta fitar dai ta zargi Sunusi Lamido da aikata wasu laifuka masu alaka da kaucewa doka wajen sarrafa kudade, da amfani da mukaminsa ba bisa ka'ida ba. Matakin da ya sanya fadar gwamnatin yanke shawarar dakatar da shi.
Kafin dakatarwar tasa, Sunusi Lamido ya fidda wasu alkaluma dake bayyana zargin bacewar wasu makudan kudaden cinikayyar danyan man kasar tsakanin ma'aikatar kudi da kuma kamfanin sarrafa man kasar NNPC. (Saminu Alhassan)