A wani ci gaban kuma kasar Sin ta ce, kasashen dake fama da tashe-tashen hankula ne ke da alhakin samar da tsare-tsaren kare hakkokin yaransu, yayin da kuma a hannu guda ake da bukatar samar da managarcin shiri na kasa da kasa, da zai samar da yanayin tsaro, da na zamantakewa ga yaran da kasashensu ke fama da tashe-tashen hankula.
Wannan tsokaci ya fito ne daga bakin mataimakin wakilin din din din na kasar Sin a MDD Wang Min, yayin zaman kwamitin tsaron majalissar da ya gudana a ranar Litinin, wanda kuma ya mai da hankali ga tattauna batutuwan da suka shafi kare hakkokin yara a lokutan yake-yake.
Ambasada Min ya kara da cewa, akwai matukar bukatar hadin kan kasashen duniya, wajen taimakawa kasashen da rikice-rikice ke addaba a fannin karfafa masu gwiwa ga batun kare yara kanana, ciki hadda batun tallafawa kasashen a fannonin kakkabe fatara, da inganta ilimin bai daya ga yara, da kuma samar da ci gaba mai dorewa. (Saminu)