Majalisar ta sanar da hakan ne a yau Talata, inda har ila take son ayyana ranar ta 13 ga watan Satumba a matsayin ranar tunawa da wadanda sojojin kasar ta Japan suka halaka a kisan kiyashin da suka aikata a birnin Nanjing a shekarun 1930.
Za a tattauna daftarin shawarar ce yayin taron kwamitin majalisar wakilan jama'ar Sin da ake gudanarwa sau biyu a wata, wanda za a gudanar daga ranar Talata zuwa ranar Alhamis.
Sojojin na Japan sun fara aikata wannan danyen aiki ne a Nanjing a ranar 13 ga watan Disamban shekarar 1937, inda suka halaka mutane sama da 300,000 cikin kwanaki 40. (Ibrahim)