in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tanzaniya ta nuna kin yarda da hukuncin kotun kungiyar kasashen Gabashin Afirka kan hanyar Serengeti
2011-09-06 14:46:52 cri
Kasar Tanzaniya ta bayyana kin amincewarta da hukuncin kotun kungiyar kasashen Gabashin Afirka, wanda ya yi watsi da nuna rashin amincewar gwamnatin kasar da karar da kungiyar kula da walwalar dabbobi ta Afirka ta shigar, don dakatar da aikin gina wata hanya mai nisan kilomita 800, da zata ratsa fitaccen gandun dajin Seregeti da ke Arewa maso Gabashin Tanzaniya.

Babban alkalin kasar Tanzaniya, ya ja kan cewar, kasarsa tana da damar gudanar da ayyukan jin dadin zaman jama'a a duk fadin iyakarta, yayin da shi kuma alkalin kotun ya dage kan cewar, duk da ikon da gwamnatin Tanzaniya take da shi na aiwatar da aiki a kasarta, ita kuma kotun tana da karfin yanke hukuncin kan ko irin wadannan ayyuka suna bisa ka'ida, kuma ana saka ran gabatar da karar a gaban kotun ta hanyar da ta dace, sannan za'a saurare ta sosai.

A ranar 10 ga watan Disamban shekara ta 2010 ne, kungiyar kula da walwalar dabbobi ta nahiyar Afirka ta ruga kotun yankin, don dakatar da aikin gina hanyar, tana mai korafin cewar, hanyar zata kassara yanayin gandun dajin, tare da ja kan cewar, gina hanyar da zata ratsa Serengeti, wanda shi ne babban gandun dajin kasa na Tanzaniya, da har ila yau ya hada iyaka da gandun dajin Maasai-Mara na kasar Kenya, ya sabawa yarjejeniyar kungiyar habaka tattalin arzikin yan Gabashin Afirka. (Garba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China