Kakakin fadar gwamnatin kasar Rueben Abati ya bayyana hakan da yake Karin haske akan lamarin ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua a Abuja babban birnin tarayyar kasar.
Mr Abati yace tuni aka umurci Malam Sanusi daya mika ragamar shugabancin bankin ga babbar mataimakiyar shi Mrs Sarah Alade,wadda zata rike kujerar har sai an gama binciken game da zargi yi ma dokoki zagon kasa,rashin bin kai'idojin tafiyar da harkokin bankin da salon mulkin da ake yi bankin.(Fatimah Jibril)