in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tsohon gwamnan jihar Kano a tarayyar Najeriya yayi kira ga masu rike da madafun ikon da su kyautata zaman rayuwar talakawa
2014-02-15 20:07:38 cri

Tsohon gwamnan jihar Kano dake arewacin tarayyar Najeriya, Malam Ibrahim Shekarau, ya gargadi 'yan siyasa masu rike da madafun iko, da suka kasa kyautata rayuwar talakawa, duba da cewa hakkokin al'ummar ya rataya a wuyan su.

Shekarau ya bayyana hakan ne a jiya Jumma'a, a gidan gwamnatin jihar Bayelsa dake birnin Yenagoa, yayin wani bikin taya gwamnan jihar, Seriake Dickson, murnar cika shekaru biyu akan mulki.

Malam Shekarau ya ce duk wani gwamna ko mai rike da mukamin siyasa, da ya maida hankali kan gina tituna, da gudanar da manyan ayyuka ba tare da kyautata walwalar jama'a ba, kamar su biyan 'yan fansho hakkokinsu, da bunkasa harkokin kasuwanci, zai hadu da fushin ubangiji.

Daga nan sai tsohon gwamnan jihar ta Kano ya jinjinawa gwamna Dickson, bisa mutunta doka da oda, da bunkasa rayuwar jama'a, da kokarinsa da yake yi na yaki da cin hanci da rashawa. (Murtala)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China