in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Faransa sun yi musayar wuta da dakarun dake dauke da makamai a babban birnin kasar Afrika ta tsakiya
2013-12-23 14:48:35 cri
A ranar 22 ga wata, kakakin hedkwatar kwamandan sojojin Faransa Pascal Georgin ya bayyana cewa, a wannan rana, sojojin Faransa sun yi musayar wuta da wasu dakaru dauke da makamai a Bangui, babban birnin Afrika ta tsakiya, ba tare da fayyace yawan mutanen da suka rasu ko suka jikkata ba.

Sojojin Faransa sun yi musayar wuta da wasu dakarun a birnin Bangui har sau biyu, musayar wuta ta farko tare da wasu mayakan tsofuwar kungiyar 'yan tawayen Seleka guda 6, sannan musanyar wuta ta biyu an yi tsakanin sojojin Faransa da wasu 'yan sari-ka-noke.

Georgin ya kuma bayyana cewa, a wannan rana, an yi zanga-zanga har sau biyu a birnin Bangui da kowace ta tara mutane kimanin 1000, yawacin masu zanga zangar sun yi ihu na nuna adawa ga sojojin kasar Faransa da suke zargi da rashin adalci cikin aikinsu na kawo zaman lafiya da kuma harbe wasu dakarun Seleka da suka yi har lahira a wannan rana. (Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China