Nesirky wanda ya bayyana hakan a ranar Talata yayin ganawar sa da manema labaru, ya ce tashin hankalin na baya bayan nan ya sabbaba mutuwar a kalla mutane 12, baya ga wasu mutanen 30 da suka jikkata.
Har ila yau ofishin na BINUCA ya nuna damuwa kan irin tasirin da tashe-tashen hankula dake ci gaba da aukuwa a kasar ka iya haifarwa a nan gaba. Don haka ofishin ya yi kira ga mahukuntan kasar da su kara azama wajen tabbatar da tsaron rayukan fararen hula, tare da tabbatar da hukunta wadanda ke da hannu a rura wutar rikici.
Har wa yau, ofishin na BINUCA ya jaddada bukatar kwamitin tsaron MDD na ganin dukkanin kungiyoyin 'yan tawayen dake kasar sun ajiye makaman su, tare da rungumar shirin sulhu domin wazar da yanayin zaman lafiya mai dorewa.
Rahotanni dai na cewa tashe-tashen hankulan da ke addabar yankunan Arewa maso Gabashin kasar a baya bayan nan, na dada haifar da koma baya ga yunkurin da ake yi na dawo da yanayin zaman lafiya da tsaro a fadin kasar, tare da jefa kusan daukacin al'ummar kasar miliyan 4 da dubu dari 6 cikin mawuyacin halin rayuwa.(Saminu Alhassan)