in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rundunar sojin saman Nigeriya sun kai samame a maboyar 'yan ta'adda a arewacin kasar
2014-02-06 16:26:52 cri
A Laraban nan 5 ga wata rundunar sojan saman Nigeriya ta sanar da kai samame a maboyar 'yan ta'adda dake jihar Borno a arewa maso gabashin kasar, daya daga cikin jihohi 3 dake karkashin dokar ta baci.

Wannan samame yana daga cikin kokarin da ake yi na murkushe wadannan kungiyoyi da suka yi kakagida a jihohin Borno,Yobe da Adamawa, in ji kakakin rundunar ta 79 na sojojin sama Chris Erondu a wata sanarwar da ya sama hannu kuma Xinhua ta samo mana.

Samamen dai ya zo kasa da awowi 24 bayan da wadansu 'yan bindiga da ake zargin 'yan fashi da makami ne suka kai hari ga 'yan kasuwa a kan titin Ngalda na jihar Yobe, abin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 19 sannan aka jikkata wadansu 5 kuma a kauyen Bara.

A cikin sanarwar, Chris ya yi bayanin cewa rundunar sojin saman sun kai samamen ne a Bulabulim, Yujiwa-Alagarno, dukkansu a garin Damboa dake jihar na Borno bayan da suka samu cikakken bayani game da wuraren da kyau.

Kakakin rundunar saman har ila yau ya bayyana cewa an samu nasara a samamen domin 'yan ta'addan sun janye jiki daga wannan yanki sai dai kuma sun shiga kasashe makwabta da suka hada da Chadi, Kamaru da Jamhuriyar Niger.

Yana mai bayanin cewa rundunar ta 79 karkashin rundunar sojin sama za su ci gaba da sa ido a garin na Maiduguri da garuruwa makwabta domin hana faruwar wani harin. (Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China