in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rundunar 'yan sanda a Najeriya ta tabbatar da mutuwar mutane 16 sakamakon harin da aka kai musu
2014-02-11 20:33:22 cri
A ranar Litinin ne hukumomin 'yan sanda a Najeriya, suka tabbatar da cewa, wasu 'yan bindiga sun halaka wasu mutane 16 a garin Maru da ke jihar Zamfara.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Lawal Abdullahi, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua ta wayar tarho cewa,wasu 'yan bindiga ne a kan babura suka halaka fararen hulan 15 da wani dan sanda guda 1.

Jami'in ya ce, 'yan bindigan sun yiwa kauyukan Tungar Rakumi,Mallamawa da kuma Kangarawa kawanya ne a daren ranar Asabar,kana suka kashe mutane 12 a kauyen Tungar Rakumi kadai,yayin da suka halaka sauran mutanen a kauyukan Mallamawa da kuma Kangarawa.

Abdullahi ya ce,maharan wadanda ke dauke da bindiga kirar AK 47,ana zaton sun kai hare-haren ne domin mayar da martani kan kashe wasu nutane 3 da ake zargi da satar shanu a makon da ya gabata.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China