140203murtala
|
Ministan wutar lantarki na tarayyar Najeriya, farfesa Chinedu Nebo ya sake tabbatar wa 'yan kasar, musamman ma kamfanoni, cewa nan ba da dadewa ba, za'a samu wadatacciyar wutar lantarki a kowane lokaci.
Farfesa Nebo ya ba da tabbaci ne a wurin taron rantsar da sabon shugaban kungiyar gamayyar 'yan kasuwa, manoma da mahakan ma'adanai ta jihar Enugu (ECCIMA).
Kamar yadda ya ce, koma-bayan da ake samu a bangaren wutar lantarki na wucin gadi ne, wanda a yanzu gwamnati ke yin iyakacin kokari domin samar da wadatacciyar wutar a kasa baki daya. Ya ce,
"Mun kammala ayyuka masu yawan gaske. Gwamnati ta fitar da kayan aikin da suka kamata domin ganin an samu wutar lantarkin da ba'a daukewa", in ji ministan.
A shekarar da ta gabata ne dai, gwamnatin tarayya Nigeriya, a kokarinta na magance rashin wutar lantarkin da ake fama da shi a fadin kasar, ta mika nauyin samar da lantarkin a hannun 'yan kasuwa, sai dai tun bayan daukar sabon matakin, jama'a da dama suke sukarsa, inda suke bayyana cewa, maimakon samun karuwar lantarkin, sai ma raguwarta da aka samu a wurare da dama. (Murtala)