in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya ya koma jam'iyyar adawa ta APC
2014-02-03 16:56:28 cri
Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Abubakar Atiku, ya sanar a ranar Lahadi koma wa jam'iyyar APC, jami'yyar adawa a Najeriya mafi girma dake neman karbe iko daga jam'iyyar shugaba Goodluck Jonathan, jam'iyyar PDP mai mulki. Mista Atiku, daya daga cikin wadanda suka kafa jam'iyyar PDP, ya bayyana cewa ya dauki wannan mataki ne bayan rangadin da ya kammala zuwa yankunan kasar inda ya samu jin ra'ayin magoya bayansa ta fuskar fagen siyasa.

Ya ce matakinsa ya biyo bayan rashin cika alkawuran da jam'iyyar PDP ta dauka da kuma babbar matsalar shugabanci da jam'iyyar ke fuskanta. Malam Atiku ya nuna cewa bayan yin shawarwari, ya dauki niyyar koma wa APC da yake ganin jam'iyya ce da za ta iya kawo babban sauyi ga kyautatuwar zaman rayuwar al'ummomin na Najeriya, tare da samun ci gaba da mai dorewa cikin kasa guda.

Jam'iyyar PDP na kan mulki tun a shekarar 1999 tun bayan mulkin wucin gadi zuwa mulkin farar hulla, ta fara fuskantar ficewar 'ya'yanta da suka hada da 'yan majalisu da gwamnoni da suka koma jam'iyyar APC domin shirya wa zabubukan shekarar 2015. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China