in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar Belgium, 'dodo mai launin ja' a nahiyar Turai
2013-11-01 16:16:08 cri


Belgium wata karamar kasa ce da ta kasance tsakanin kasashen Holland, Jamus, da kuma Faransa. Duk da cewa fadin kasar ba shi da girma, amma kungiyar wasan kwallon kafanta tana da karfi da kwarewa sosai. A gasar rukunin A wato rukuni na daya na yankin Turai, na neman samun izinin halartar gasar cin kofin duniya ta shekarar 2014, kungiyar Belgium ta ci wasanni 8, ta kuma yi kunnen doki da abokiyar karawa karo guda, inda kuma ta samu saka kwallaye 17 cikin raga, matakin da ya sa ta zama ta farko cikin rukuninta, ta kuma samu damar kara nuna bajinta a gasanni dake matsayin koli.

Hakika, kungiyar ta kasa samun damar halartar zagayen karshe na gasannin cin kofin duniya da suka gudana a shekarar 2006 da ta 2010, amma a wannan karo, ana sa ran ganin ta nuna cikakken karfi, da taka rawar gani a gasar da za a yi a kasar Brazil, ganin yadda kungiyar ke da fitattun 'yan wasa masu kwarewa sosai. Yanzu bari mu waiwayi yanayin da kungiyar Belgium take ciki a da, da dalilin da ya sa ta farfadowa sosai a 'yan shekarun nan.

Idan mun dubi jadawalin jerin kungiyoyi da hukumar FIFA ta fita na watan Oktobar bara, za mu ga cewa Belgium na a matsayi na 40, wato tana biye da Ukrain, da Norway, da dai sauransu. Kana a shekarar 2007, kungiyar Belgium ta taba fadowa zuwa matsayi na 71 a duniya. Ta wannan matsayi za a iya tunanin yadda jama'a masu sha'awar wasan kwallon kafan kasar suke bakin ciki matuka ga yanayin da kungiyar ke ciki. Amma a yanzu, Belgium ta riga ta daga matsayinta zuwa matsayi na 6, a jerin kungiyoyin kasashen duniya baki daya. Yanzu haka, ana samun fitattun 'yan wasa da yawa cikin kungiyar kasar ta Belgium. Kamar yadda wata tashar yanar gizo ta Internet ta kasar Jamus ta yi hasashe, an ce kudin neman sayen 'yan wasa daga kungiyar, idan an lasafta dukkan 'yan wasan kungiyar 25, za a ga ya kai kimanin Euro miliyan 355. Wannan jimilar ba ta ma shafi dukkan 'yan wasan kungiyar ba, idan aka yi la'akari da cewa ThomasVermaelen, wanda ke taka leda a kulob din Arsenal, da Radja Nainggolan dake taka kwallo a Cagliari, dukkan su na jiyya a yanzu haka. Idan kuwa aka kara da 'yan wasan 2, to, kudin neman sayen 'yan wasan kungiyar Belgium zai kai Euro miliyan 385, wanda ya kasance a mataki na 4 a duniya, bayan na kasashen Spain, da Jamus, da Brazil.

Idan muka sake duban tsarin wasan Primier na zakarun nahiyar Turai, za mu iya ganin yadda kasar Belgium take samun kwararrun 'yan wasa da yawa, ciki hadda Marouane Fellaini na Manchester United, Eden Hazard na Chelsea, Kompany na Manchester City, da dai sauran manyan 'yan wasa, da suka kai 12, dukkansu 'yan kasar ta Belgium, wadanda ke taka rawar gani a gasar ta Premier League.

Idan mun dubi alkaluman da aka fitar kan yawan kwallayen da 'yan wasan Premier League suka saka a raga, daga farkon kakar wasa ta 2012-13 har zuwa yanzu, za mu ga 'yan wasan Belgium din nan su 12 , sun ci kwallaye 80, jimilar da ta wuce maki 74, da 'yan wasan kasar Faransa 36 suka samu a gasar ta Premier. Ta haka ma kadai, za mu iya ganin kwarewar 'yan wasan kasar ta Belgium. Amma na san masu sauraronmu za su yi tambayar cewa, yaya kungiyar Belgium, wadda ta kasa shiga zagayen karshe na gasannin cin kofin Turai na shekarun 2004, da 2008, da 2012, wadda kuma ba ta samu tikitin shiga gasannin cin kofin duniya da suka gudana a shekaru 2006 da 2010 ba, kwatsam a shekarar 2013, ta kai ga zama daya daga cikin kungiyoyi mafi karfi a duniya?

1 2
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China