Museveni ya bayyana hakan ne ranar Lahadi, yayin wata ganawar sirri da 'yan jam'iyyar da ke mulki a'yan majalisun dokokin kasar.
Shugaba Museveni ya ce,za a hukunta masu goyon bayan luwadi,yayin da aka soke wani sashi na dokar da ta bukaci a aiwatar da hukuncin kisa kan masu aikata wannan laifi a baya,inda a wannan lokaci za a yanke wa duk wanda aka kama yana aikatawa wannan laifi hukuncin da ya kai na daurin rai da rai.
Tun a shekarar 2009 ne aka gabatar wa majalisar dokokin kasar wannan doka, wadda ta samu amincewar baki dayan 'yan majalisar.
A ranar Lahadi ne kuma shugaban kasar Amurka, Barack Obama ya bayyana rashin jin dadinsa game da shirin shugaba Museveni na aiwatar da wannan doka,inda ya yi gargadin cewa,wannan yunkuri zai kara dagula dangantaka tsakanin Amurka da kasar ta Uganda,tare da haifar da koma baya ga 'yan kasar. (Ibrahim)