in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yan majalisar jam'iyyar NRM sun tsaida Museveni a zaben shugaban kasa na 2016 a Uganda
2014-02-11 10:51:24 cri

Yan majalisar jam'iyyar NRM dake mulki a kasar Uganda, sun tsaida shugaba mai ci Yoweri Museveni a matsayin 'dan takararsu a zaben shugaban kasa na shekarar 2016.

A cikin wata sanarwar da aka fitar a ranar Litinin daga fadar shugaban kasa dake Kampala, 'yan majalisar sun jadadda a yayin babban taronsu babbar rawar da shugaba Museveni ya taka a matsayin shugaban jam'iyya da shugaban kasa wajen tabbatar da zaman lafiyar kasa.

Sun bayayya cewa, sun dauki wannan mataki ta yin la'akari da rawar da mista Museveni ya taka domin tabbatar da zaman lafiya, tsaro, demokaradiyya da kawo babban sauyi kan zaman al'umma da na tattalin arziki da sauransu, tare da bayyana fatansu na ganin ya kasance 'dan takara guda a shekarar 2016, kuma za su ba shi goyon baya yadda ya kamata, in ji wannan sanarwa. Sai dai kuma a cewar sanrwar, har yanzu Museveni bai mai da martani ba kan wannan tayi na 'yan majalisa.

Idan aka amince da takararsa a shekarar 2016, wannan shi ne karo na biyar da mista Museveni ya rike da wani sabon wa'adi na shekaru biyar na shugabancin kasa.

Mista Museveni ya hau karagar mulki a shekarar 1986 bayan tawaye na tsawon shekaru biyar. A shekarar 1996, ya lashe zaben shugaban kasa tare da fara wa'adinsa na shekaru biyar na farko a matsayin zababben shugaban kasa. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China