in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban CAR yana tuntubar 'yan tawayen Uganda na LRA
2013-11-22 09:49:27 cri

Shugaban kasar jamhuriyar Afrika ta Tsakiya CAR Michel Djotodia a ranar Alhamis din nan 21 ga wata ya tabbatar da cewa, yana tuntubar shugaban 'yan tawayen kasar Uganda na Lord's Resistance Army wato LRA kuma suna tattauna yadda za su kawo karshen tawayen da ake yi mafi tsawo a nahiyar Afrikan.

A wani bangaren kuma gwamnatin ta sanar da cewa, an bai wa kungiyar LRA karkashin jagorancin Joseph Kony wani daman zama a kasar na wucin gadi a garin Yalinga na kasar Afrika ta tsakiyar.

A farkon wannan makon ne jami'an MDD suka nuna damuwarsu cewa, gwamnatin rikon kwarya ta jamhuriyar Afrika ta Tsakiya na tattaunawa da kungiyar 'yan tawayen LRA, wadda kotun hukunta masu laifuffuka ta duniya ICC take nema ruwa a jallo ga shugabanta bisa zargin aikata laifukan yaki.

Djotodia ya ce, Kony da sauran dubban magoya bayansa suna son mika wuya idan har aka amince da sharuddansu.

Idan ba'a manta ba, Michel Djotodia ne ya jagoranci kungiyarsa na Seleka wajen hambarar da gwamnatin kasar Afrika ta Tsakiya karkashin shugaba Francois Bozize a watan Maris, abin da ake ganin a matsayin juyin mulki, sannan kuma shi Djotodian ya amince da kafa gwamnatin wucin gadi ta watanni 18 karkashin shugabancin babbar kungiyar adawa da gwamnati ta CEEAC a watan Afrilu.

Sai dai kuma an ci gaba da fuskantar fadace-fadace masu tsanani tsakanin mayakan Seleka da magoya bayan hambararren shugaban kasar Bozize, abin da ya yi sanadiyar asarar rayukan mutane fiye da 50 a fadan da aka yi ranar 26 ga watan Oktoba kawai a garin Bouar da ke arewacin kasar. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China