in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun DRC sun fatattaki 'yan tawayen ADF na Uganda
2014-02-11 11:01:42 cri

Shugaba Yoweri Museveni na Uganda, ya ce, dakarun sojin jamhuriyar dimokaradiyyar Congo DRC, sun samu nasarar fatattakar mayakan kungiyar 'yan tawayen ADF ta Uganda, mai hedkwata a Beni da ke gabashin yankin Kivu.

Cikin wata sanarwa da fadar shugaba Museveni ta fitar a ranar Litinin 10 ga watan nan, shugaban ya ce, takwaransa na Congo Joseph Kabila ya tabbatar masa da cewa, 'yan tawayen ADF din sun arce daga sansanin nasu dake Beni ne, sakamakon sumamen da sojin Congon suka kaddamar.

Don haka shugaba Museveni ya godewa takwaransa na Congo bisa wannan namijin kokari da dakarunsa suka yi.

A ranar 16 ga watan Janairun da ya gabata ma dai, sai da sojojin kasar Congo suka kaddamar da wani sumame a yankin na Kivu, da nufin dakile tasirin mayakan na ADF mai alaka da kungiyar Al-Qaida.

Shi dai wannan tsari na fatattakar magoya bayan kungiyoyin 'yan tada kayar baya, wani yunkuri ne da kasashen yankin ke yi, da nufin kauda mayakan sa kai daga gabashin jamhuriyar dimokaradiyyar Congo, wadanda aka yi amannarsu ne sanadiyyar tashe-tashen hankulan dake addabar yankin tsahon lokaci. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China