in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Uganda na yaki tare da sojojin Sudan ta Kudu, in ji shugaban Uganda
2014-01-16 11:00:24 cri

Shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni ya bayyana a ranar Laraba cewa, sojojin Uganda na yaki kafada da kafada tare da rundunar sojojin kasar Sudan ta Kudu domin karbe yankunan dake karkashin 'yan tawaye.

A cikin wata sanarwa da fadar shugaban kasar Uganda ta fitar, shugaba Museveni ya bayyana cewa, sojojin Uganda da na SPLA sun fatattaki 'yan tawayen dake biranen Bentiu da Malakal.

"A ranar 13 ga watan Janairu, sojojin SPLA da wasu dakarun rundunar sojojinmu sun gwabza kazamin fada tare da mayakan 'yan tawaye a wurin dake da kimanin kilomita 90 daga birnin Juba, kuma mun karya lagonsu sosai." in ji mista Yoweri Museveni a gaban shugabannin shiyyar a yayin wani zaman taron kasashen yankin babban tafki a birnin Luanda na kasar Angola.

Abin bakin ciki shi ne, an samu asarar rayuka sosai daga wajen 'yan tawaye, haka ma daga bangarenmu, an samu mutuwa da jikkata, Har zuwa jiya da yamma, gwamnatin Sudan ta Kudu tare da taimakon sojojinmu, ta karbe garin Jemeza, in ji mista Museveni.

A ranar Talata ce, majalisar dokokin kasar Uganda ta ba da goyon bayanta ga tura sojojin kasar zuwa Sudan ta Kudu.

Haka kuma gwamnatin Uganda ta tabbatar da cewa, ta tura sojojinta bisa amincewar gwamnatin Sudan ta Kudu. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China