'Yan sanda a nan take suka kaddamar da farautar 'yan fashin bayan da aka kai masu rahoto kuma sakamakon haka aka gano su sannan ba tare da bata lokaci ba aka harbe su a wannan dare.
Mataimakin kwamishinan 'yan sanda a Lusaka,Nelson Phir yayi bayanin cewa a lokacin da aka gano su an samu manyan bindigogin AK47 guda biyu tare da su da kuma wata karamar motar shiga.
Mr Nelson Phir yayi bayanin cewa an samu shaidu masu kwari dake nuna cewa wadannan mutane su ne suka yi fashin a safiyar ranar laraba a ma'aikatan hakar kwaru dake wajen birnin Lusaka abinda yayi sanadin jikkatar Sinawa 7, daga baya daya daga cikin su ya mutu a asibiti saboda mummunan raunin da ya samu. (Fatimah Jibril)