in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mahukunta a Zambiya sun kuduri aniyar habaka matakin ilimi a kasar
2011-09-09 13:37:01 cri

Kafar yada labarai ta kasar Zambiya (ZANIS) ta ruwaito cewar, gwamnatin kasar ta bayyana kudurinta na daga matakin ilimi a tsakanin magidanta da yara a kasar.

Kamar yadda wani safiyon kiwon lafiyar iyali da aka gudanar a kasar Zambiya ya nuna, magidanta kimanin miliyan daya da dubu dari uku ne suke fama da karancin ilimi a kasar. Kwatankwacin kashi talatin da uku da digo takwas na magidanta a Zimbabwe.

Daniel Bowasi, sakataren lardin Lusaka ya bayyana cewar, gwamnati tana mayar da hankali wajen daga matsayin ilimi, sabili da ta fahimci cewar, mutane masu ilimi suna ba da taimako mai ma'ana ga batutuwan da suka shafi siyasa, al'umma da bunkasar tattalin arziki.

A jawabin da ya gabatar, albarkacin bikin ranar ilimi ta kasa da kasa, jami'in ya ce gwamnati ta na ci gaba da ba da damar aiwatar da nagartattun manufofin bunkasa ilimi.

Daniel Bowasi ya ce, gwamnati na da alhakin samarwa, hadawa da kula da ayyukan yakar jahilci da ke da burin habaka ilimi a tsakanin manya. Kafar ta ZANIS ta bayyana taken bikin na bana matsayin "Ilimi dan jama'a". (Garba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China