Mataimakin sakatare janar na MDD a kan 'yancin bil adama Ivan Simonovic shine ya bayyana hakan lokacin da yake kammala ziyararsa ta kwanaki hudu a kasar, inji mai Magana da yawun MDD Martin Nesirky, yayin jawabi da aka saba yiwa 'yan jarida kullum.
Simonovic ya bayyana cewa ko da yake hali da ake ciki a Bangui babban birnin kasar ya 'dan inganta, babu wani abin tasiri a wajen babban birnin kuma babu doka, inji Nesirky wanda ya kara da cewa jami'in ya nuna damuwa dangane da cin zarafi na jima'i a kasar.
An samu barkewar tashin hankali a watan disamba da ya wuce a Afirka ta tsakiya, wacce ta shafe shekaru tana fama da rashin tsaro da fadace-fadace, wato lokaci da 'yan tawayen Seleka suka kai hare-hare.
An cimma yarjejeniyar zaman lafiya a watan Janairu to amma a watan Maris 'yan tawayen sun sake kwace birnin Bangui, inda suka tilasa shugaba Francois Bozize ya tsere.
Fadace-fadace na baya bayan nan ya kara kawo illa ga harkokin hidima a kasar da kuma kara tabarbarewar yanayin zaman bil-adama, inda hakan inji jami'in na MDD ya matukar shafi kusan dukkan jama'ar kasar da yawansu ya kai miliyan 4.6, wadanda rabinsu yara kanana ne. (lami Ali Mohammed)