in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hadin gwiwar Sin da Ghana ta fannin samar da wutar lantarki
2013-10-14 18:03:53 cri


Cikin 'yan shekarun baya, tattalin arzikin kasar Ghana ya bunkasa cikin sauri, sai dai matsalar karancin wutar lantarki ta kan yi wa bunkasuwar tattalin arzikin tarnaki. Amma a halin yanzu, masana'antar samar da wutar lantarkin nan mai suna Kpone da ke karkashin kamfanin Sunon Asogli Power(Ghana) da kamfanin samar da makamashi na Shenzhen na kasar Sin da asusun bunkasa Sin da Afirka suka zuba jari kamfanin tana taka muhimmiyar rawa ta bangaren samar da wutar lantarki a kasar ta Ghana.

Bisa ga shirin, masana'antar samar da wutar lantarki ta Kpone za ta iya samar da wutar lantarki da ya kai Kilowatts dubu 560, kuma an fara aiki da rukuni na farko na na'urorin masana'antar daga ranar 12 ga watan Oktoban shekarar 2010, wadanda suke samar da wutan da ya kai sama da KW.H biliyan guda a kowace shekara. Baya ga haka, rukuni na biyu na na'urorin masana'antar za su iya samar da wutan da ya kai Kilowatts dubu 360, wadanda har aka sanya su cikin shirin bunkasa wutar lantarki na kasar Ghana, kuma yanzu haka ake share fagen aiki da su.

Bayan da aka fara aiki da masana'antar a watan Oktoban shekarar 2010, masana'antar ta taimaka matuka a fannin sassauta matsalar karancin wutar lantarki da ke damun kasar ta Ghana. A game da rawar da masana'antar take takawa ta bangaren masana'antun samar da wutar lantarki a Ghana, Mr.Chu Shuntang, shugaban ofishin asusun bunkasa kasar Sin da Afirka da ke kasar Ghana, ya bayyana cewa, "masana'antar samar da wutar lantarki ta Kpone ba kawai ta inganta aikin samar da wuta a kasar Ghana ba, hatta ma ta samar da dimbin guraben aikin yi ga al'ummar kasar."A shekarar 2011, ministan harkokin waje na kasar Ghana ya cewa Chu Shuntang, saurin bunkasuwar tattalin arzikin kasar da ta kai na farko a kasashen Afirka a waccan shekara ba zai rasa nasaba da taimakon da masana'antar ta Kpone ta samar ba.

A game da damuwar da wasu mutane da kafofin yada labarai na kasashen yammaci da na Afirka suka nuna game da yadda kasar Sin ke hada gwiwa da kasar Ghana da sauran wasu kasashen Afirka, sakataren hukumar kula da makamashin kasar Ghana, Alfred Ofosu Ahenkorah ya nuna cewa, "ba na ganin hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da Ghana ta fannin samar da wutar lantarki a matsayin wani na'u'i na mulkin mallaka ne kamar yadda wasu ke damuwa a kai, alal misali, yadda kamfanin Sunon Asogli Power (Ghana) ke hada gwiwa da mu zuba jari ne kawai kamar yadda sauran wasu kasashe ke yi a wurinmu, wato hadin gwiwa ne ta fannin zuba jari, kuma kasar Ghana ma ba za ta nuna bambanci ga masu zuba jari na kasar Sin da na sauran kasashe a manufofin da take aiwatarwa ba."

Bunkasuwar aikin samar da wutar lantarki, da ci gaban tattalin arziki. Ghana wadda tattalin arzikinta ke saurin bunkasa ita ma ta fahimci muhimmancin bunkasa wannan aiki na samar da wuta. Don haka, ta sanya rukuni na biyu na aikin kafa na'urorin samar da wuta a masana'antar Kpone cikin shirin kasar gaba daya na samar da wuta. An ce, bayan da aka kammala wasu ayyuka na bincike da tantancewa da suka shafi aikin, kuma hukumar kula da makamashi ta Ghana ta amince da aikin, za a fara aikin kafa na'urorin a tsakiyar shekarar 2014, kuma za a fara aiki da su a shekarar 2015. Zuwa lokacin, masana'antar ta Kpone za ta samar da karin taimako ga ci gaban tattalin arziki da zaman al'umma a kasar ta Ghana.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China