in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi harbe-harbe a Kinshasa, babban birnin kasar Kongo(Kinshasa)
2013-12-31 15:46:29 cri


A ranar 30 ga watan Disamba na shekara ta 2013, an yi harbe-harbe a wurare da dama a Kinshasa, babban birnin kasar Kongo(Kinshasa), sakamakon haka wasu dakaru masu dauke da makamai sun kwace babban ginin hedkwatar gidan talebijin din kasar, kuma tare da garkuwa da wasu ma'aikata. Wannan dai ya sanya mutane damuwa da halin da ake ciki a kasar sabo da bai kai wata guda ba da gwamnatin kasar da dakarun da ke adawa da gwamnati wato M23 suka daddale yarjejeniyar shimfida zaman lafiya, amma sai ga shi an sake samun harbe-harbe dake nuna wani sabon salon arangama da juna.

Bisa labarun da muka samu daga hukumar 'yan sanda na birnin Kinshasa, an ce, dakaru da yawansu kusan dari rike da bindigogi sun kai hare-hare a filin jirgin sama, da sansanin soja, da gidan talibijin na kasar da ke Kinshasa, babban birnin kasar. Har dakarun sun samu nasarar kwace babban ginin hedkwatar gidan talebijin kasar, tare da kama wasu ma'aikata don yin garkuwa da su. A halin yanzu, sojojin gwamnati sun sake mamaye wadannan wurare, inda suka harbe dakaru a kalla 40 har lahira, amma babu farar hula ko sojojin gwamnati da suka rasu a cikin wadannan harbe-harbe.

Bidiyon gidan talibijin kafin aka katse watsa shirye shirye ya nuna, ma'aikata biyu a firgice, wasu dakaru suna rike da wuka akan su inda maharani ke nuna korafin su na adawa da shugaban kasar Joseph Kabila.

Wadannan dakarun sun ce su ne mabiyan Gideon Mukungubila, wanda ya yi takarar zabe da shugaba mai ci Joseph Kabila a shekarar 2006.

Mukungubila ya yi suka kan yarjejeniyar shimfida zaman lafiya da gwamnatin Kongo(Kinshasa) ta daddale tare da kungiyar da ke adawa da gwamnati wato M23 a watan Disamba na shekara ta 2013, Gideon Mukungubila ya yi zargin cewa, bisa matsyin da makwabciyar kasar wato Uganda ta bayar, gwamnatin Kabila ta ba da fifiko ga 'yan kabilar Tutsi da ke nasaba da kungiyar M23. A cikin wata wasikar da ya rubuta ga jama'ar kasar Mukungubila ya nuna damuwa ga makomar kasar Kongo(Kinshasa), kuma ya nuna kiyayya ga kasar Uganda. Sabo da a tarihi, Uganda ta taba kai hari a kasar Kongo(Kinshasa), kuma har kullum ta kan nuna goyon baya ga dakarun da ke adawa da gwamnatin kasar Kongo(Kinshasa).

Amma kakakin bangaren 'yan sanda na birnin Kinshasa Colonel Mwana ya bayyana cewa, ko da yake dakarun sun ce su mabiyan Gideon Mukungubila ne, duk da haka ba a iya tabbatar da hakan ba. Har yanzu ana bincike hakikanin halin da ake ciki. Ya yi nazari cewa, wadannan dakaru matasa ne marasa aikin yi a birane, dauke da tsoffin makamai, kuma yawan dakarun bai yi yawa ba, sabo da haka da wuya a iya cewa ko suna da buri a fannin siyasa, watakila suna son kawo barazana ne kawai gabannin shigowar sabuwar shekara.

A birnin Kinshasa, mazauna na cikin fargaba, inda suka rufe shagunansu, kuma kowa ya zauna a gida ba fita. An kafa dokar-ta-baci a sansanin soja da babban ginin gidan talibijin din kasar, inda aka yi harbe-harbe mai karfin gaske, 'yan sanda masu kwantar da tarzoma suna sintiri a kan tituna. A halin yanzu dai bangaren 'yan sanda yana kokarin ceton mutanen da aka yi garkuwa da su.

Bayan harbe-harbe a Kinshasa, sojojin gwamnati sun yi musayar wuta da wasu dakaru na daban da ke jihar Katanga da ke bakin iyakar kasa a tsakanin Kongo(Kinshasa) da Zambiya. A yayin da ake harbe-harbe a Kinshasa, shugaba Kabila yana rangadin aiki a jihar Katanga, amma hakan bai zama barazana a gare shi ba.

Sakamakon rashin zaman karko a fannin siyasa, tare da lalacewar tattalin arziki cikin dogon lokaci a kasar Kongo(Kinshasa), a Kinshasa, babban birnin kasar, ya kasance matattaran matasa da ba su da ayyukan yi, inda suke rike da makamai, suna kashe mutane, da aikata fashi, da kai farmaki kan mazaunan wurin. Bayan da aka yi jita jita cewa wai shugaba Joseph Kabila zai yi gyare-gyare kan tsarin mulkin kasa, kuma zai ci gaba da zama shugaban kasar bayan shekara ta 2016, an kara samun tashe-tashen hankula a birnin Kinshasa, inda ake zargin wadannan matasa marasa aikin yi ne suka da aikata hakan. (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China