A ranar Talatan nan 11 ga wata, kasar Zimbabwe ta bukaci taimako na kudin dalar Amurka miliyan 20 daga kasashen waje da kungiyoyin kasa da kasa domin ta ceto mazauna kauyuka dake kusa da wata madatsar ruwa dake dab da ballewa a yankin kudu maso gabashin kasar.
Ministan kasar mai kula da ma'aikatar kananar hukumomi, ayyukan al'umma da tsara gidaje Ignatius Chombo ya shaida wa wakilan kasashen waje da na kungiyoyin kasa da kasa dake Harare, babban birnin kasar Zimbabwe cewa, mutane 20,000 mazauna dab da madatsar ruwan Tokwe-Mukorsi dake gundumar Masvingo na fuskantar barazanar ambaliya.
Makonnin da suka shude, ana ta tabka ruwan sama mai karfi ya kawo rudani a wuraren da a da aka san suna matukar karancin ruwa. Madatsar ruwar Tokwe-Mukorsi da wata kamfanin Italiya take ginawa ta cika ta batse da ruwa, abin da ke barazana ga dumbin al'umma mazauna kusa da wajen.
Mr. Chombo ya yi bayanin cewa, kudaden da ake fatan samu, za'a yi amfani da su wajen samar da kayayyakin abinci, matsuguni, ruwa mai tsafta da sauran bukatun yau da kullum ga mazauna wannan wuri tare da sauya musu matsuguni. Sannan kuma gwamnati ta yi kiyasin cewa, barazanar da sauran mutane 40,000 da suke zauna dab da matsadar ruwan ke fuskanta na da 'dan sauki.
Shugaban kasar Robert Mugabe dai a ranar Lahadin nan ya rigaya ya kaddamar da dokar ta baci a wannan yankin domin a samu kai dauki cikin gaggawa ga mazauna dake cikin bukata. (Fatimah)