Fiye da mutane 15000 ne na bukatar agajin gaggawa a yankunan kudu maso gabashin kasar Nijar, bayan wata mabaliyar ruwa da batsewar wani tafkin dake wurin ta janyo, a cewar wata hukumar aikin ba da agajin jin kai ta MDD a ranar Talata.
Gwamnatin kasar Nijar tana jagorancin ayyuka na kai agajin gaggawa tare da taimakon kungiyoyin ba da agaji na MDD, in ji kakakin MDD Martin Nesirky da ke ambato kalaman hukumar daidaita harkokin ayyukan jin kai ta majalisar dinkin duniya OCHA, shi kuma ya bayyana cewa, a halin yanzu, an riga an rarraba abinci fiye da tan 90 ga mutanen da wannan matsala ta shafa a wadannan yankuna na kasar Nijar. (Maman Ada)