in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 4000 suka rasa muhalli sakamakon ambaliyar ruwa a jihar katsina ta Najeriya
2013-09-24 10:03:49 cri

A kalla mutane 4,000 ne suka rasa muhallinsu sakamakon ambaliyar ruwa a kananan hukumomi 17 a jihar Katsina ta tarayyar Najeriya.

Babban sakatare a hukumar kula da ba da agajin da tsugunar da jama'a ta jihar Hassan Rawayau wanda ya tabbatar da hakan ga wakilin Xinhua a ranar Litinin ya ce, ambaliyar ruwa duk da hakan ta yi sanadiyar asarar dukiyoyi na miliyoyin naira na kudin Najeriya.

Sai dai a cewarsa, duk da wannan asarar barnan da ambaliyar ta yi bai kai na shekarar da ta wuce ba, wadda mutane sama da 10,536 suka rasa muhallinsu, yana mai danganta wannan nasarar ga sakamakon wayar da kan jama'a da ma'aikatar muhalli ta yi game da hatsarin dake cikin ambaliyar ruwa.

Ya ce, banda duba iya barnan da ambaliyar ta yi domin ba da taimakon da ya kamata gwamnatin jihar da hukumomin da abin ya shafa sun fara ba da agajin da ya kamata ga wadanda ambaliyar ta rutsa da su, musamman a kananan hukumomin Kankia, Charanci da Faskari, Sai dai a bayanin da ya yi, ambaliyar bana ta fi shafar karamar hukumar Kusada, in ji jami'in. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China