Ruwan sama da aka yi kamar da bakin kwarya a Bujumbura, babban birnin kasar Burundi a cikin daren Lahadi zuwa Litinin sun yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da 50, yawanci kananan yara tare da jikkata daruruwan mutane bayan kuma asarar dukiyoyi, in ji ofishin ministan tsaron jama'ar kasar.
An fara ruwan saman da misalin karfe goma na dare bisa agogon wurin. Ambaliyar ruwan da suka kawararo daga tsaunuka zuwa babban birnin ta haddasa barna a yankunan dake arewa masu yammacin Bujumbura. Bayan asarar rayuwa, ruwan sun lalata gidaje da motoci, haka kuma sun janyo matsalolin ta fuskar kiwon lafiya ta hanyar lalata wuraren banhaya dake kusa da madatsun ruwa na shayar da gonaki dake kewayen Bujumbura.
Haka kuma ruwan saman sun lalata hanyoyi da babbar hanyar kasa dake hada Bujumbura da sauran jahohin arewacin kasar da hanyar dake zuwa filin saukar jiragen saman kasa da kasa dake birnin Bujumbura. Asibitocin Bujumbura sun yi fama da karuwar mutanen da suka ji raunaku, in ji hukumonin da abin ya shafa. Ministan tsaron jama'a Gabriel Nizigama ya bayyana cewa, tuni gwamnatin kasar ta sanar da zaman makoki da daukar nauyin ba da kulawa ga wadanda suka jikkata. (Maman Ada)