Kasar Zimbabwe ta samu rancen kudi daga kasar Sin a ranar Talata na dalar Amurka miliyan 23,3 domin taimakawa kasar bunkasa gine-ginenta a yankunan karkara.
Ministan kudi da cigaban tattalin arzikin kasar Zimbabwe, Patrick Chinamasa tare da jakadan kasar Sin dake kasar ta Zimbabwe Lin Lin sun rattaba hannu kan wannan yarjejeniyar a Harare, babban birnin wannan kasa dake kuriyar nahiyar Afrika.
Mista Chinamasa ya bayyana cewa, wadannan kudade za su shiga wajen gina asibitoci, makarantun faramare da sakandare a yankunan da suka amfana tsarin karbe gonaki domin baiwa 'yan kasa.
Gwamnatocin kasashen biyu sun amince da yin aiki tare a yayin da suke kokarin cimma yarjejeniyar da ta shafi wannan taimakon kudi a cikin watanni uku masu zuwa, ofishin jakadancin kasar Sin dake Zimbabwe zai cigaba da ba da tallafi ga sauran ayyuka da tsare-tsare a cikin wannan kasa. (Maman Ada)