in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zimbabwe ba za ta kori 'yan kasashen waje dake gudanar da kananan kasuwanci a kasar ba
2013-12-30 14:27:55 cri

Gwamnatin kasar Zimbabwe ta ce, ba za ta kori 'yan kasashen waje dake gudanar da kananan kasuwanci daga cikin wasu fannonin sana'o'in guda goma ba, a cewar wani ministan kasar Zimbabwe domin kawar da fargabar 'yan kasashen waje masu shaguna a kasar game da irin dokar da aka taba amfani da ita wajen karbe gonaki yau fiye da shekaru goma da suka gabata, a cewar jaridar Sunda Mail mallakar gwamnatin kasar a ranar Lahadi.

Ministan kula da makomar matasa da hukumomin kasar Zimbabwe, Francis Nhema ya bayyana cewa, ba za'a ba da wata dama ba ga wani 'dan kasar Zimbabwe da ya jaroranci wasu masana'antun dake hannun 'yan kasashen waje a kasar Zimbabwe.

Yan kasashen waje dake gudanar da wasu kebabbun ayyukan kasuwanci, za su cigaba da gudanar da harkokinsu yadda ya kamata domin sun yi muhimmin aiki wajen samar da ayyuka a lokacin da kasar ta fuskanci wasu matsalolin tattalin arziki da kudi.

A shekarar 2010, kasar Zimbabwe ta sanya hannu kan wata dokar dake ba da gatanci kawai ga 'yan kasar Zimbabwe wajen gudanar da harkokin kasuwanci a wasu fannoni goma sha hudu wadanda suka hada da noma, sufuri, ba da hayar motoci, sana'ar aski, sana'ar ba da hayar gidaje, sarrafa taba da sauransu. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China