A wannan rana kuma, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hong Lei ya bayyana cewa, kasashen Sin da Philippines, kasashe ne da suka rattaba hannu kan yarjejeniya game da tekun kudu, kuma kamata ya yi su bi alkawarin da suka dauka cikin yarjejeniyar a tsanake, haka nan kuma Hong Lei ya jaddada cewa, Sin ba ta amince da matakan da Philippines za ta dauka na neman sulhuntawa a kotun kasa da kasa ba, kuma ta bayyana adawar ta karara ga wannan lamari. Hong Lei ya kuma jaddada cewa, Sin ta tsaya kan ra'ayinta cewa, ya kamata a tsaya ga bin tsarin yin shawarwari wanda akasarin kasashen da ke wannan yanki na nuna goyon baya a halin yanzu, kuma Sin za ta ci gaba da kokari don kiyaye zaman lafiya da karko a yankin tekun kudu, da tsayawa tsayin daka wajen tabbatar da mulkin kai da moriyar kasar.(Bako)