in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kudurin da majalisar dattawan Amurka ta zartas kan batun yankin teku dake kudancin kasar Sin ba shi da tushe
2011-06-29 11:15:43 cri

Ranar Talata 28 ga wata, a wajen wani taron manema labarai da aka shirya, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Mista Hong Lei ya ce, kudurin da majalisar dattawan kasar Amurka ta zartas dangane da batun yankin teku dake kudancin kasar Sin ba bisa gaskiya ba ce, kuma ba shi da tushe ko kadan, kasar Sin tana fatan 'yan majalisar dokokin Amurka za su kara gudanar da ayyukan da za su taimaka ga tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a wannan yanki.

Mista Hong Lei ya ce, kwanan baya, majalisar dattawan Amurka ta zartas da wani kuduri, inda ta ce, kasar Sin na nuna fin karfi a yankin tekun dake kudancin kasar, kamata ya yi bangarori daban-daban su daidaita duk wani irin sabani ta hanyar lumana, da nuna goyon-baya ga sojojin Amurka wajen daukar matakan tabbatar da 'yancin yin zirga-zirga a yankin tekun.

Hong ya ci gaba da cewa, abu mafi muhimmanci a batun yankin teku dake kudancin kasar Sin shi ne, takaddamar da ake yi tsakanin wasu kasashen dake kewaye da wannan yankin teku dangane da samun ikon mallakar wasu tsibirai da kokarin kowace kasa na shata iyakokinta a tekun, kamata ya yi a warware takaddamar ta hanyar yin shawarwari kai-tsaye tsakanin kasashen da abun da ya shafa. Hong Lei ya ce, takaddamar ba ta taba kawo illa ga 'yancin zirga-zirgar jiragen ruwa a yankin teku dake kudancin kasar Sin ba, kasar Sin ta bada shawarar cewa, a warware sabani da takaddama ta hanyar yin shawarwari cikin lumana.(Murtala)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China