in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta kaddamar da sabuwar tashar hakar man fetur a tekun Nanhai
2012-05-09 15:54:17 cri

Yau Laraba 9 ga wata, kasar Sin ta kaddamar da sabuwar tashar hakar man fetur wadda ta kasance tasha ta zamani da kasar Sin ta kera da kanta. Nau'ra mai lamba 981 dake tashar ta kutsa karkashin kasa har zuwa tsayi mita 1500. Lamarin da ya alamanta cewa, hakar man fetur da kasar Sin take samu a teku ya ci gaba.

Wannan shi ne karon farko da kamfanin man fetur na kasar Sin ya kaddamar da aikin hakar man fetur da gas mafi zurfi a teku. Abin da ya sa, Sin ta zama kasa ta farko dake hakar man fetur da gas a tekun Nanhai da kanta. A gun bikin da aka yi a wannan rana, babban direktan kamfanin Wang Yilin ya nuna cewa, an kaddamar da na'ura mai lamba 981 a tekun Nanhai, abin da ya sheda cewa, Sin ta fara aikin hakar man fetur a wuri mafi zurfi cikin teku, kuma ya habaka ci gaban da aka samu a wannan fanni. Wanda kuma zai taka rawar wajen tabbatar da yin makamashi yadda ya kamata, sa kaimi ga tsarin inganta karfin kasar ta wannan hanya, tare da kiyaye ikon mulkin sararin teku na kasar Sin.(Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China