Hong ya ce, tun daga farkon wannan shekara, kasar Sin da kasashen membobin kungiyar tarayyar kasashen kudu maso gabashin Asiya sun shirya tarurukan manyan jami'ai guda 2, inda bangarori daban daban suka cimma daidaito kan aiwatar da yarjejeniyar da aka kulla wadda ta kayyade matakan da za a dauka dangane da batun yankin tekun dake kudu da kasar Sin.
Ban da haka kuma, bangarorin da batun da ya shafa na kokarin tsara wata doka game da haka. A cewar Hong, kasar Sin a nata bangare tana fatan ganin sauran kasashe za su girmama kokarin da kasar Sin da kasashen kudu maso gabashin Asiya suka yi, sa'an nan su kara daukar wasu matakai da za su taimakawa kara aminci da tabbatar da kwanciyar hankali.
Kakakin ya kara da cewa, kasar Sin tana sane da cewa kasar Amurka ta taba bayyana matsayinta na 'yan ba ruwan mu dangane da cece-kuce da ake yi kan ikon mallakar tekun dake kudu da kasar Sin, don haka kasar Sin na fatan ganin Amurka za ta tsaya kan maganarta, kana ta kara gudanar da wasu ayyukan da za su taimaka wajen samar da zaman lafiya a wannan yankin. (Bello Wang)