in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanin man fetur na Shell ya rufe reshensa a kasar Nijeriya
2011-12-22 10:56:46 cri

Ranar Laraba 21 ga wata, reshen Nijeriya na kamfanin man fetur na Shell ya sanar da cewa ya rufe wannan reshe saboda abkuwar malalar mai a wurin hakar man fetur na Bonga a tekun dake kudu maso gabashin kasar Nijeriya.

A cikin wata sanarwa, kamfanin ya ce, ya sami rahoto a ran 20 ga wata da ya nuna cewa, ya sami hadarin malalar mai da yawansa ya kai kasa da ganga dubu 40. Yanzu kamfanin ya dakatar da aikin hakar mai bisa dalilin tsaron lafiyan mazauna yankin.

A cikin sanarwar, kamfanin ya nemi gafara bisa ga abkuwar lamarin, kuma ya ce ya riga ya kwashe man fetur da ya malala tare da daukan matakin ko ta kwana.

An ba da labari cewa, wurin hakar mai na Bonga na da nisa kilomita 120 daga gabar Nijeriya, wanda yake iya samar da mai har ganga dubu 200 a ko wace rana.(Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China