140117-rundunar-sojojin-kiyaye-zaman-lafiya-ta-kasar-sin-karo-na-farko-na-tafiyar-da-aiki-a-Mali-bilkisu
|
A yamacin ranar Alhamis da ta gabata, rukuni na biyu na rundunar sojojin kiyaye zaman lafiya da kasar Sin ta tura karo na farko ta isa Bamako, babban birnin kasar Mali. Rundunar ita ce rundunar sojojin tsaro ta farko da kasar Sin ta aika zuwa wata kasar waje tun bayan da ta soma shiga ayyukan kiyaye zaman lafiya na MDD a shekarar 1990. A yanzu haka dai, rukuni na farko na rundunar ya riga ya gudanar da ayyukansu a Mali har tsawon kwanaki sama da 40. Sojojin sun samu yabo sosai daga wajen jami'an MDD sakamakon yadda suke ayyukansu.
A safiyar ranar 25 ga watan Disamba na shekarar 2013, an samu tashin boma-bomai a kudu maso gabashin sansanin rundunar sojojin kiyaye zaman lafiya ta kasar Sin dake Mali.
A cikin minti 1 da dakika 32 bayan tashin boma-bomai, dukkan sojojin rundunar an kafa su a sassa daban daban don daukar mataki. Bisa binciken da aka yi an tabbatar da cewa, an harba rokoki guda biyu ne, daya bai wuce kogin Nijer ba, dayan kuma da an harba a wurin dake da nisan kilomita daya daga sansanin sojojin kasar Sin.
Rundunar sojojin kiyaye zaman lafiya da kasar Sin ta aike zuwa Mali, ita ce rundunar soja ta farko da kasar ta aika zuwa wata kasar waje don gudanar da ayyukan tsaro. An girke su a yankin Gao, inda suke fama da fashewar boma-bomai da zafi mai tsanani, Tun daga watan Nuwamba na shekarar da ta wuce, an kai farmakin ta'addanci har sau 16 a yankin, ciki har da fashewar boma-bomai da aka ajiye a cikin motoci, da sace mutane, da kuma kisan gilla. Akwai 'yan ta'adda fiye da 500 da suka saje da fararen hula, wadanda suka buya a yankin Gao, inda a wasu lokuta su kan kai farmaki ga sansanin rundunar sojojin kiyaye zaman lafiya ta Sin.
Lallai abubuwan da sojojin kasar Sin suke yi a nan ba atisayen soja ba, wadannan sojojin kiyaye zaman lafiya suna nan zahiri kasar Mali.
Wani soji na rundunar, Ma Zhao ya gaya wa wakilinmu cewa,
"A cikin wata daya da muka iso nan kasar Mali, abin da ya fi dame ni shi ne kalubale wajen tsaro da kullum ke kasancewa a kewayenmu, dole ne mu yi shirin ko ta kwana a ko da yaushe. Ba mu saba da yanayin nan ba, sannan muna fuskantar kalubalolin da yanzu ba mu ma san su ba."
Tun bayan da 'yan kundumbala suka iso yankin Gao na kasar Mali a farkon watan Disamba na bara, duk da farmakin ta'addanci da mawuyacin halin da suke fuskanta, sun kammala ayyukan kafa sansanoni, raba sojoji zuwa kungiyoyi daban daban, yin atisayen soja game da gudanar da aikin gaggawa cikin dare da sauransu. A waje guda kuma, sun kafa sansanin wucin gadi mai fadin muraba'in mita dubu 20, kana sun karbi kayayyakin soja fiye da ton 1700.
A ranar 14 ga watan Disamba na bara, an tayar da wani farmakin ta'addanci na kunar bakin wake a birnin Kidal dake da nisan kilomita fiye da 400 daga sansanin sojojin kiyaye zaman lafiya na kasar Sin, a sakamakon haka, sojojin kiyaye zaman lafiya na kasar Senegal guda 2 sun mutu, yayin da wasu 7 suka jikkata. A wannan rana, babban kwamandan dake kula da harkokin yankin gabas na tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD da ke Mali (MINUSMA), Mamadou ya ba da umurni ga ofishin jagoranci na tawagar, da sojojin kiyaye zaman lafiya da su yi koyi da yadda sojojin kasar Sin suke gudanar da ayyukan tsaro, don karfafa karfin tsaro. Ana iya cewa, sojojin kiyaye zaman lafiya na kasar Sin dake Mali sun nuna wa kasashen duniya jaruntaka da taurin rai da Sinawa suke da shi.
Jagoran rundunar, Zhang Geqiang ya bayyana cewa,
"Wadannan rukunoni uku sun kasance rundunar sojojin kiyaye zaman lafiya da kasar Sin ta tura karo na farko zuwa kasar ta Mali, a waje guda sun kasance rundunar ayyukan tsaro ta farko da kasar Sin ta aika zuwa kasashen waje. bai kamata mu bata sunan gwamnati da jama'ar kasarmu ba, za mu nuna wa duniya wata rundunar sojoji ta babbar kasa dake sauke nauyin dake kanmu." (Bilkisu)