Mr. Brahimi da ya ke bayani ga manema labarai ya ce ya gana da wakilan 'yan adawa da na gwamnati daban daban a ranar jumma'an, sannan yana fatan a yau asabar da gobe lahadi kamar yadda suka amince za'a hadu gaba daya a zaure daya.
A safiyar wannan rana Ministan harkokin wajen Syria Walid al-Moallem ya shaida ma Brahimi cewa idan ba'a tattauna wani abin a zo a gani ba lokacin zaman ranar asabar, to wakilan gwamnatin Syria za su bar Geneva saboda rashin wani shirin da kuma halin ko oho da bangaren adawa suka nuna a tattauanawar.
A ranar jumma'a har ila yau, Louay Safi kakakin babbar kungiyar adawa na SNC ta zargi gwamnatin Syria da rashin nuna fatan alheri da kuma kokarin kaucewa hanyar siyasa ta warware batun kasar.
Bangaren adawa ya nuna karara cewa, zasu zauna a tattauna ne kawai bisa ga sanarwar bayan taron Geneva na farko kan zaman lafiya da aka yi a shekarar 2012, wanda suka yi imanin cewa ya bukaci a kafa gwamnatin wucin gadi kuma Shugaba Assad ya sauka daga mukamin sa.(Fatimah Jibri)