in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban ki-moon ya bukaci gwamnatin Siriya da bangaren adawa na kasar da su tattauna
2014-01-23 11:10:27 cri

A ranar 22 ga wata, a birnin Montreux da ke kasar Switzerland ne sakatare janar na M.D.D. Ban Ki-moon ya shugabanci taron kasa da kasa game da batun Siriya, inda bangarori daban daban suka yi muhawara sosai game da mukamin shugaban kasar Bashar Al-Asad.

A gun taron, shugaban tawagar kasar Siriya, kuma mataimakin firaministan kasar, kana ministan harkokin wajen kasar Walid Muallem ya yi dogon jawabi, inda ya jaddada cewa, tsige shugaba Al-Asad shi ne sharadin da tawagar Siriya ba za ta amince ba. Muallem ya zargi dakarun bangaren adawa da aikata laifuffuka kan fararen hula, kana ya musunta bayanai marasa tushe da kafofin yada labaru na kasashen yammacin duniya suka yada labaru game da gwamnatin Siriya.

A gun taron shugaban bangaren adawa na Siriya Ahmad Jarba ya zargi gwamnatin Asad da aikata laifuffukan yaki, inda ya bukaci tawagar Siriya da ta amince da shirin tsige Asad daga mukaminsa.

A gun taron, sakataren harkokin wajen kasar Amurka John Kerry ya ce, bai kamata a sanya shugaba Asad cikin jerin sunayen gwamntatin wucin gadin kasar ba. Ya kuma soki gwamnati Asad. A nasa bangare, ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergie Lavrov ya bayyana cewa, ya kamata bangarorin biyu na kasar Siriya su warware batun Siriya cikin lumana, kuma bai kamata sauran kasashe su sanya baki cikin harkokin cikin gidan kasar Siriya ba.

Bayan taron, a gun taron manema labaru da Ban Ki-moon da manzon musamman na M.D.D. da kungiyar hadin gwiwar kasashen AL game da batun Siriya Lakhdar Brahimi suka halarta, Ban Ki-moon ya ce, bayan aka shafe har tsawon shekaru 3 ana rikici a kasar ta Syria, abu ne mai wuya a sa wakilan gwamnatin Siriya da na bangaren adawa su zauna tare, kuma lamarin na da ma'anar musamman sosai. Game da hali mai tsanani da ake ciki a kasar Siriya, ya kamata a yi shawarwari don kawo karshen rikicin, kuma ya kamata a yi amfani da wannan dama, don lalubo bakin zaren warware matsalar a siyasance. (Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China