in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin DRC da 'yan tawayen M23 sun koma teburin shawarwari
2013-04-09 13:37:43 cri

A wani mataki na kawo karshen dauki-ba-dadi dake faruwa tsakanin dakarun gwamnati da na 'yan tawayen M23 a gabashin DRC jamhuriyar dimokaradiyyar Congo, bangarorin biyu sun koma teburin shawarwari a Kampala, babban birnin kasar Uganda.

Taron tattaunawar da aka fara ranar Litinin 8 ga watan nan, wanda kuma Uganda ke jagoranta, ya zo gabar da kwamitin tsaron MDD ke shirin tura dakarun wanzar da zaman lafiya, wadanda za su yi aiki kafada-da-kafada da ragowar sojojin dake ayyukan sa kai a kasar. Duka dai da nufin mai do da yanayin tsaro, da kwanciyar hankula a wannan yanki.

Har ila yau wannan tattaunawa da a baya aka fara cikin watan Disambar bara, na zuwa bayan da wani tsagi na kungiyar ta M23 suka balle, bayan samun wata kazamar rashin jituwa a cikin kungiyar.

Duk dai da matakin aika karin dakaru da MDD ta kuduri aniyar dauka, ministan tsaron kasar Uganda Crispus Kiyonga, ya tabbatarwa manema labaru cewa, kungiyar ta M23 na nuna sha'awa ga hawa teburin shawarar.

Bugu da kari, Kiyonga ya yiwa kungiyar ta M23 alkawarin cewa, ko kusa, ba za a kai musu hari ba, muddun dai sun yarda da ci gaba da tattaunawa, yana mai bayyana cewa, daukar matakai na siyasa, na da matukar muhimmanci ga burin dawo da zaman lafiya a kasa.

A nasa bangare, Rene Abandi, wanda ke magana da yawun kungiyar M23, bayyana rashin jin dadinsu ya yi, don gane da sabon matakin da MDD ta dauka, na tura dakarun da za su yaki da 'yan kungiyar tasu, duk kuwa da amincewar da suka yi na bin hanyoyin siyasa domin warware rashin jituwarsu da tsagin mahukunta.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China