Bayan abkuwar lamarin, 'yan sandan kasar, sun kange hanyoyin da ake bi zuwa kurkukun, kana sun kewaye wurin.
Akwai membobin kungiyar Boko Haram da dama a cikin wannan kurkuku.
Ministan kula da harkokin dokokin shari'a na kasar Nijer Marou Amadou ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu, ba a san ko akwai alaka tsakanin wannan lamari da lamarin fashewar boma-boman kunar bakin wake da ya faru a ranar 23 ga watan Mayun da ya gabata a kasar ba. (Zainab)