A cewar wannan sanarwa ta gwamnatin kasar Nijar da ta fito bayan wani zaman taron ministoci da aka shirya a ranar Laraba a birnin Yamai, kamar yadda aka tsara bisa tushen takardun hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu, ton hamsin na nama ne kasar Nijar za ta rika tura wa kasar Guinee-Equatoriale sau biyu a ko wane wata.
Tuni manyan 'yan kasuwa na kasashen biyu suka yi shirin rattaba hannu kan takardun kwagilar kasuwanci da za su kasance wani matakin aza harsashi, da kuma matakan yadda za'a rika biyan kudi, da yadda za a fitar da su bisa amincewar bangarorin biyu.
Wata tawagar aiki ta ma'aikatar kiyon kasar Nijar za ta isa birnin Malabo nan bada jimawa ba, domin kara azama kan ayyukan da aka tsaida bisa tushen yarjejeniyoyin da kasashen biyu suka sanya wa hannu. (Maman Ada)