Madam Kididiatou Dandobi ta yi wannan jawabi a yayin bikin ranar nakasassu ta kasa karo na 21 da aka gudanar a ranar Laraba, bisa taken "Karfin bada kulawa ga fasahar nakasassu, wani muradi na cigaban kasar Nijar".
A cewar wannan jami'a, kasar Nijar na daya daga cikin kasashen shiyyar yammacin Afrika da ta tanadi makaman dokoki don kare nakasassu kuma kasa ta farko ta sanya hannu kan yarjejeniyar kare mutunci da 'yancin nakasassu a ranar 24 ga watan Yunin shekarar 2008. (Maman Ada)