Bayanai na cewa, kamfanin ya dauki wannan mataki ne sakamakon gazawar kamfanin na cimma yarjejeniya tsakaninsa da gwamnatin Nijar din .
Kamfanin na Areva dai ya shafe sama da shekaru 40 yana hako ma'adinin Uranium a Arlit dake arewacin kasar ta Nijar ta hannun rassansa guda biyu wato SOMAIR da COMINAK, inda yarjejeniyar da sassan biyu suka sanya hannun ta kawo kasrhe a ranar 31 ga watan Disamban shekara ta 2013.
Sai dai sassan biyu sun shafe sama da wata guda suna tattaunawa don ganin an kulla wata sabuwar yarjejeniyar shekaru 10, ko da yake gwamnatin Nijar din ta nace cewa, wajibi ne a inganta sabuwar yarjejeniyar, inda kamfanin na Aeva yake amincewa da duk wani tayin karin haraji bisa dalilin cewa, farashin ma'adinin ya fadi a kasuwannin duniya. (Ibrahim)