in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhu na MDD ta yi tir da harin kunar bakin wake a Jamhuriyar Nijar
2013-05-25 16:49:00 cri
A jiya jumma'a 24 ga wata kwamitin sulhu na MDD ta yi suka da kakkausar murya game da harin kunar bakin waken da aka kai a garin Arlit da Agadez dake arewacin kasar Nijar suna kiran shi da ta'addanci ganin yadda ya hallaka mutane da dama sannan wassu suka samu rauni.

Mambobin kwamitin 15 da suka nuna aihinin su tare da mika ta'aziyar su ga 'yan uwan wadanda wannan mummanan aiki ya ritsa da su,har ila yau sun jaddada bukatar dake akwai na zakulo wadannan miyagun da suka aikata wannan barna domin a hukunta su,tana mai kira ga daukacin jihohin kasar da su hada kai da gwamnatin kasar wajen ganin hakan ya tabbata.

Haka kuma mambobin kwamitin sun jaddada bukatar dake akwai na amfani da dukkan hanyoyi kamar yadda yake a kundin MDD da kuma dokar kasa da kasa musammam a game da 'yancin dan adam,'yan gudun hijira da kuma ayyukan jin kai sannan da ayyukan 'yan ta'addan da ke kawo barazana ga zaman lafiya da tsaro. (Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China