Gwamnatin Nijar dai da abokin kasuwacinsa na Areva dake hakar ma'adinan uranium tun yau da kusan shekaru hamshin a arewacin kasar, za ta sake tattauna kwangilar dake tsakaninta da Areva yau da kusan shekaru goma domin ganin ta cimma wata sabuwar kwangila cikin dogon lokaci tare da wannan kamfani na kasar Faransa da za ta kasance mafi alfanu ga kasar Nijar. Hukumomin kasar Nijar na ganin cewe babu daidaici kan huldar kasuwancinta tare da Areva, lamarin dake nuna cewa kasar Nijar bata samun wata babbar moriya. (Maman Ada)