Koda ya ke masu aikin ceto ba su tantance yawan wadanda suka jikkata sanadiyar tashin bam din ba.
Bugu da kari basaraken yankin Idrissa Timka, ya tabbatar da abkuwar lamarin, yayin da ya ziyarci gwamnan jihar Borno Kashim Shettima a garin Maiduguri, babban birnin jihar ta Borno, inda ya ce, ana zaman dar-dar a yankin.
Sai dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin, amma ana zargin kungiyar nan ta Boko Haram,da ke haifar da barazanar tsaro a kasar da ke yammacin Afirka da kai harin. (Ibrahim)