Shugabannin sun bayyana cewa yarjejeniya ta siyasa da aka sanya hannu kanta a birnin Lebreville ranar 11 ga watan Janairu 2013 itace zata ci gaba da zama matashiyar tsarin siyasa a yayin lokacin shirin mika mulkin.
Haka zalika sun amince a kafa gwamnatin rikon kwarya ta kasa (NTC) da kuma amincewa da zabin hukumar dangane da wa zai zama shugaban kasar Afirka ta tsakiya.
Shugabannin kungiyar ECCAS har wa yau yayi kira a kafa kotun shirin mika mulki wacce zata tabbatar da doka da oda, warware gardama ta siyasa, sanar da sakamakon zabe da kuma rantsar da sabon shugaban kasar.
Shugabannin dake ganawa a N'djamena sun yi kira ga kasa da kasa su ba da hadin kai ga kokarin dawo da zaman lafiya da tsaro a kasar Afirka ta tsakiya.
Sun jaddada cewa suna masu nuna cikakken amincewa kan kwamiti dake bin diddigin aiwatar da yarjejeniyar ta Libreville, karkashin shugaban kasar Congo, Dennis Sassou Nguesso, suka kuma yi kira ga kwamitin ya bada hadin kai ga tsarin mika mulkin.
A yayin ganawar, sun amince da cewar akwai bukatar a kafa wata kungiyar kasa da kasa da ta kunshi kungiyoyin yankuna da na kasa da kasa inda kasar Afirka ta tsakiya zata kasance mamba, sannan kungiyar zata kunshi abokan aiki daban daban na kasar.
Wannan kungiya dai itace za'a dorawa nauyin hado kudade da ake bukata don gudanar da shirin mika mulkin.(Lami Ali Mohammed)