Ya kamata a jinkirta yanke hukunci ga shugabannin Afirka dake kan mulki, in ji shugaban Afirka ta Kudu
A ranar Litinin 14 ga wata, shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma ya bayyana cewa, kasarsa tana goyon bayan bukatar da kungiyar AU ta mika wa kotun manyan laifukan duniya ta jinkirta yanke hukunci ga shugabannin kasashen Afirka dake kan mulki.
Shugaba Zuma ya ce, yanzu bai kamata a yanke hukunci ga shugabannin kasashen Afirka dake kan mulki ba amma za a iya yanke musu hukunci bayan kammala wa'adin mulkinsu. Idan kuma har sun aikata laifi, ya kamata a jinkirta yanke musu hukunci, ta yadda za su kammala aikinsu yadda ya kamata.(Fatima)