Da farko, jakada Deng ya isar da gaisuwar shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, Zhang Dejiang ga mista Mark, tare da nuna masa godiya kan goyon bayansa ga aikin ofishin jakadancin Sin a Nijeriya. Jakada Deng ya bayyana cewa, a cikin shekaru uku da suka wuce, tare da taimakon mista Mark kai tsaye, majalisun dokokin kasashen biyu sun kara yin musayar ra'ayi tsakaninsu, hakan ya kasance wani muhimmin kashi na dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a tsakaninsu. Yana fatan mista Mark zai ci gaba da ba da kulawa da kuma nuna goyon baya ga hadin gwiwa tsakanin Sin da Nijeriya, ta yadda za a sa kaimi ga bunkasa hulda tsakanin kasashen biyu zuwa wani sabon mataki.
A nasa bangare kuma, mista Mark ya bukaci jakada Deng da ya isar da gaisuwarsa ga mista Zhang Dejiang tare da nuna godiyarsa ga jakada Deng sabo da kokarinsa na sa kaimi ga sada zumunci, musamman ma ga hadin gwiwa tsakanin majalisun dokokin kasashen biyu, da fatan zai ci gaba da mai da hankali kan bunkasuwar Nijeriya, da kasancewa abokin jama'ar kasar har abada. (Fatima)