in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bankin duniya zai baiwa CAR tallafin dala miliyan 100
2014-01-24 10:08:34 cri

Bankin duniya ya bayar da sanarwar cewa, zai yi kokarin samar wa jamhuriyar Afirka ta Tsakiya (CAR) tallafin kudi dala miliyan 100, ta yadda za ta farfado bayan yakin da ya wargaza kasar a cikin 'yan watannin nan.

Bankin da ke da matsuguni a birnin Washington na kasar Amurka, ya bayyana hakan ne ranar Alhamis, inda ya ce, zai samar wa kasar wannan tallafi ne daga asusunsa na kota-kwana, don taimakawa kasar maido da muhimman ayyukan gwamnati da samar da abincin da ake bukata, kayayyakin kiwon lafiya da sauran muhimman abubuwa da jama'arta ke bukata.

Mataimakin shugaban bankin mai kula da harkokin nahiyar Afirka, Makhtar Diop, ya ce, al'ummar jamhuriyar Afirka ta Tsakiya na fuskantar mummunan bala'i a tarihi, al'amarin da ke matukar bukatar tallafin gaggawa daga al'ummomi kasa da kasa.

An sanya jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a matsayin kasar da ta fi ko wace kasa fama da talauci a duniya, inda ta shafe lokaci mai tsawo tana fama da rikice-rikcen siyasa da sauran bala'o'i.

Bayanai na nuna cewa, tashin hankalin da kasar ta fuskanta a watan Disambar shekarar 2013, ya kara dagula al'amura, inda yanzu haka kusan rabin al'ummarta ke matukar bukatar agaji. Kusan mutane miliyan 1 ne suka bar gidajensu, rabi daga cikin na zaune a Bangui, babban birnin kasar.

A 'yan makonnin masu zuwa ne, bankin duniyan zai kara goyon bayan wani shirin samar da abinci a kasar da nufin rage radadin da al'ummomin da suka bar gidajensu ke sha da kuma yadda bangaren aikin gona ya tabarbare a lokacin da rikice-rikice suka abkawa kasar. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China