in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nijar ta kwashe 'yan kasarta dake Afrika ta Tsakiya
2014-01-07 10:23:47 cri

Ganin yadda rikicin tsaro ke ta'azzara a yanzu haka a kasar Afrika ta Tsakiya CAR, da kuma nuna damuwa kan bazuwar tashe-tashen hankali da harin da aka kai ga wadanda ba su ji ba su gani ba, gwamnatin kasar Nijar ta dauki niyya tun daga ranar Jumma'ar da ta gabata ta shirya aikin kwashe 'yan kasarta da aka kiyasta yawansu zuwa fiye da 770 dake zaune a kasar Afrika ta Tsakiya.

Kimanin 'yan Nijar 300 da suka hada da mata da yara kanana tuni suka iso gida a cikin wata jigilar musamman da aka yi da jiragen sama guda biyu, tare da tura su zuwa kauyukansu na asali, haka kuma gwamnatin kasar ta kafa wani kwamitin musamman domin kula da wannan aiki.

A cikin wata sanarwa, gwamnatin Nijar ta kwantar da hankalin al'ummar kasar cewa, ta dauki dukkan matakan da suka wajaba na kwashe dukkan 'yan Nijar 771 da aka yi rajista a kasar Afrika ta Tsakiya.

Wannan aiki na kwashe 'yan Nijar dake Afrika ta Tsakiya, an shirya shi tare da taimakon kungiyar kasa da kasa game da 'yan gudun hijira (OIM), reshen tsare-tsare na MDD, kungiyar Red Cross, sojojin kasar Faransa dake cikin tawagar SANGARIS a Afrika ta Tsakiya da kuma tawagar MISCA. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China